An ceto wata budurwa mai shekaru 25 da mahaifinta ya kulleta a daki tsawon shekaru biyar

0 511

Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence a Jihar Jigawa sun ceto wata budurwa mai shekaru 25 da mahaifinta ya kulleta a daki tsawon shekaru biyar tana shan wahala.

An samu nasarar ceton ta ne, bayan wata mata mai shekaru 50 mai suna Safiya Mustapha ta fallasa yanda ake cigaba da tsare budurwar, inda ta kai rahoton ga hukumomi cewa an tsare matar ne tun tana da shekaru 20 da haihuwa.

Safiya Mustapha, wadda ta yi yunkurin ceto budurwar na zaune ne a kusa da gidan mahaifin budurwar da aka tsare.

An kuma gano cewa wani mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Musbahu Basirka, na daya daga cikin wadanda sukayi kokari wajen ceto budurwar da abun ya shafa.

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da lamarin da kuma yadda aka yi nasarar ceto ta, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya ce mahaifin na budurwar ya dauki wannan matakin ne biyo bayan wani mafarki da ba’a bayyana ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: