An ceto wani yaro dan shekara 4 daga masu garkuwa da mutane ne a jihar Kano

0 111

Rundunar ‘yansanda a Jihar Kano ta tabbatar da ceto wani yaro dan shekara hudu tare da cafke wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar.

A cewar Haruna, rundunar ‘yansandan da ke sa ido ta kama wadanda ake zargin ne a yau Asabar a Karamar Hukumar Gwarzo da ke jihar.

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, karkashin jagorancin CSP Kabiru Isah Kangiwa, ta samu gagarumar nasarar ceto wani yaro mai shekaru hudu da aka yi garkuwa da shi, Muhammad Nasir Jamilu.

An sace wanda aka yi garkuwa da shi ne daga Unguwar Sharada, aka garzaya da shi Garin Gwarzo, Karamar Hukumar Gwarzo, Jihar Kano, inda aka yi garkuwa da shi  sannan kuma suka nemi kudin fansa Naira miliyan 10.

Sanarwar ta kara da cewa, “Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta yaba wa tawagar da suka sa ido kan yadda suka nuna kwarewa da kuma daukar matakin gaggawa, wanda ya kai ga nasarar ceto yaron ba tare da an cutar da shi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: