Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin hadin baki da kisan kai a garin Hadejia.
Kakakin rundunar, SP Shiisu Adam, ya bayyana cewa waɗanda ake zargi sun hada da Malam Adamu Aliyu, da Malam Mukhtar Abdulmumin, da Malam Nafiu Ibrahim, kuma ana zargin su da damfarar wani matashi mai suna Ahmad Abdullahi naira 400,000 kafin su hallaka shi tare da jefar da gawarsa a cikin kogi.
An ce bayan aikata kisan, sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar, amma daga bisani jami’an tsaro suka cafke su tare da dawo da su Najeriya domin fuskantar hukunci.
A wani samame na daban, rundunar ta kama wani matashi da laifin satar babur mai kimanin darajar naira dubu dari shida, tare da cafke wani mutum da ya yi yunkurin harbin wata mata da bindiga saboda ya zarge ta da haddasa ciwon da ‘yarsa ke fama da shi.