Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke sama da mutane 53 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makami, masu sana’ar sayar da makamai, da masu safarar mutane da kuma barayi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Tijjani Abdullahi shine ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai na farko a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Dutse babban birnin jihar jiya alhamis.
Ya bayyana cewa uku daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da sace wani dan kasuwa a kauyen Kwaimawa da ke karamar hukumar Dutse.
A cewarsa, yayin da Mutum 10 daga cikin wadanda ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sai kuma Mutum 25 da ake zargin su da laifin sata, sai kuma Mutum uku da ake zargin su da aikata fashin mota, da kuma uku wadanda ake zargin barayin wayar hannu ne.
CP Tijjani ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta kama wani da ake zargi da ke sana’ar sayar da makamai ba bisa ka’ida ba a kauyen Dutse Kwari da ke karamar hukumar Ringim.
Haka nan akwai mutane biyu da ake zargi da safarar mutane, da satar babura guda bakwai a kananan hukumomin Dutse, Maigatari, da Kazaure. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da jama’a wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar.