An bukaci mazauna jihar Jigawa da su kula da matakan kariya domin dakile ambaliyar ruwa

0 289

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta bukaci mazauna jihar Jigawa da su yi taka-tsan-tsan tare da kula da matakan kariya domin dakile ambaliyar ruwa.

Daraktan hukumar NOA a jihar, Malam Ahmad Ibrahim, ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakinsa, Sara Ogodo, ta fitar a jiya Litinin a Dutse.

Ya ce kiran ya kasance wani muhimmin Gargadi ne kan Ambaliyar Ruwan, wanda ya nuna cewa akwai yiwuwar jihar Jigawa za ta fuskanci ruwan sama a makonni masu zuwa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ibrahim ya bayyana cewa, rahoton cibiyar FEWS ta ma’aikatar muhalli ta tarayya kan hasashen ambaliyar ruwa ya nuna cewa ruwan sama mai karfi na iya haifar da ambaliya a garuruwan Miga, Ringim, Hadejia da kuma Dutse babban birinin jihar.

Ya kuma ja hankalin jama’a da su rika taka-tsan-tsan, wajan wayar da kan jama’a ta yadda za a shawo kan ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: