An bayar da kwangilar gina sabuwar gadar da ambaliya ta lalata a Hadejia

0 250

Hukumar gyaran hanyoyin mota ta kasa ta bada kwangilar gina gada a wani bangare na hanyar motar Hadejia zuwa Gamayin da ambaliyar ruwa ta lalata.

A jawabinsa wajen kaddamar da aikin a kauyen Wailare, jami’in shiyya na hukumar Injiniya Hussaini Abubakar yace an bada kwangilar ne ga kamfanin Dan Adida, kuma ana san kammalawa cikin watanni biyu masu zuwa.

Yace Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne ya samo aikin bisa la’akari da muhimmancinsa ga tattalin arzikin jihohin Jigawa da Bauchi da Yobe da kuma Borno.

Sanata Ibrahim Hassan Hadejia

A sakonsa zuwa wajen bikin kaddamarwar, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ta bakin mai bashi shawara na musamman akan ilimin gaba da sakandire, Muhammad T. Muhammad, yace bayar da kwangilar zai dafawa kokarin gwamnatin jihar na gyaran titunan da ambaliyar ruwa ta lalata a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: