An bada umarnin aike da karin jami’an tsaro zuwa babban hanyar Abuja Kaduna

0 165

Babban safetan ‘Yan sanda na kasa Kayode Egbetokun ya bada umarnin  aike da karin jami’an tsaro zuwa babban hanyar Abuja Kaduna duba da karuwar matsalar tsaro a yankin.

Sawaba Radio ta rawaito cewa ‘Yan bindiga sunyi garkuwa da gwamman mutane matafiya a hanyar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘Yan sandan Najeriya , ACP Olumuyiwa Adejobi  ya fitar a yau,yace an aike da jami’an tsaron ne domin inganta tsaro a yankin.

Babban safetan ‘Yan sanda na kasa Mista Egbetokun ya umarci mataimakin safetan ‘Yan sanda Mista Ede Ekpeji da ya sanya ido kan jami’an tsaron da aka aike da su hanyar.  Ya bayyana bukatar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen tabbatar da tsaro, inda ya bukaci mazauna yankunan da su kasance masu lura sosai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: