An amince da shekaru 16 a matsayin mafi karanci ga dalibai da ke neman shiga Jami’a

0 195

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta amince da shekaru 16 a matsayin mafi karanci ga dalibai da ke neman shiga Jami’a.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya sanar cewa za a fara daukar dalibai masu shekaru 16 a makarantun gaba da sakandare ne daga shekarar 2025.

Ministan ya sanar da haka ne a Abuja a wurin taron Masu Ruwa da Tsaki kan harkar shiga manyan makarantun, wanda Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Kasa ta shirya.

Ya sanar da rage shekarun zuwa 16 ne bayan mahalarta taron sun tayar da hayaniya a lokacin da aka bayyana musu cewa shekaru 18 shi ne mafi karanci da doka ta kayyade domin shiga manyan makarantu.

An yayin taron Hukumar JAMB ta sanar da 140 a matsayin mafi karancin maki don shiga jami’o’i a shekarar 2024.

Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya kara da cewa maki 100 ne mafi karanci ga masu son shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha da Kwalejojin Ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: