An aike da jami’an sa ido domin kai rahoton duk wata alamar bullar cutar kwalara a Jigawa

0 178

Kwamishinan lafiya na jihar Jigawa, Dakta Abdullahi Kainuwa ya ce ma’aikatar ta aike da jami’anta kan sa ido domin kai rahoton duk wata alamar bullar cutar kwalara a jihar. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi ga manema labarai kan kokarin gwamnatin jihar na rahoton bullar cutar kwalara a wasu jihohin kasar nan. Dokta Kainuwa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar ta, kuma fara wayar da kan jama’a domin rigakafin da kuma kaucewa yaduwar cutar a jihar. Dokta Kainuwa ya ci gaba da cewa, kawo yanzu babu rahoton bullar cutar kwalara a jihar jigawa, kuma suna daukar duk matakan da suka dace domin dakile duk wata bullar cutar a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: