An ɗage sauraron ƙarar Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara zuwa 2 ga Satumba

0 376

Kamar yadda jaridar BBCHausa ta ruwaito, tace “kotu a jihar Kano da ake arewa maso yammacin Najeriya ta ɗage sauraron ƙarar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa 2 ga Satumban 2021.

A ranar Laraba ne Alkali Ibrahim Sarki Yola ya ɗage sauraron ƙarar bayan da aka yi zama na biyu tun fara shari’ar a birnin Kano.

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a faɗin ƙasar ba ma jihar Kano kaɗai ba.

Mai Shari’a Sarki Yola ya ce ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take”.

Karanta cikakken bayanin a maballin kasa;

https://www.bbc.com/hausa/labarai-58257573

Leave a Reply

%d bloggers like this: