An ƙirƙiri asusu na kimanin $100Bn don ingantawa da kuma adana abubuwan tarihi a Najeriya

0 110

Ministar Al’adu, Hannatu Musa-Musawa, ta bayyana ƙirƙirar asusun faɗaɗa tattalin arziki na dala biliyan 100 don inganta da kuma adana abubuwan tarihi na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Hannatu Musawa wanda ta samu wakilcin Daraktan Masana’antu da Kayayyakin Al’adu, Rev. Ben Ugo, a wajen bikin Ojude Oba na 2024 a jiya Talata, ya amince da bambancin al’adu na ‘yan Nijeriya, inda ya ce gwamnatin tarayya na kokarin ganin kasar nan ta zama cibiyar al’adu zuwa nan da shekarar 2030.

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya bayyana cewa, bikin da ya zama abin ban sha’awa ga masu yawon bude ido, alama ce wacca take nuna hadin kan al’umma.

Yayin da yake godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa nuna sha’awar fadada bikin, musamman sanya bikin a cikin abubuwan tarihi na UNESCO, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don bunkasa al-adun kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: