Amurka da Birtaniya da Canada sun gargaɗi ‘yan kasar su da ke zaune a Nijeriya kan batun zanga-zanga

0 258

Wasu manyan ƙasashen duniya irin su Amurka da Birtaniya da Canada sun gargaɗi ‘yan kasar su da ke zaune a Nijeriya su yi taka-tsantsan a yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasar a farkon watan gobe.

A sanarwar da ƙasashen suka fitar daban-daban sun yi kira ga ’ya’yansu su ɗauki matakai na kauce wa samun kansu a cikin zanga-zangar domin kare lafiyarsu.

Sanarwar tace, wasu rahotannin kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, mai yiwuwa a yi zanga-zanga a faɗin Nijeriya daga yau, 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga Agusta, 2024. Bisa la’akari da abubuwan da suka faruwa a baya, wannan zanga-zangar za ta ƙunshi toshe hanyoyi, da wuraren binciken ababen hawa da haddasa cunkoson ababen hawa da taho-mu-gama, a cewar ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya.

Don haka ne Amurka ta buƙaci ‘ya’yanta su guji shiga taron jama’a, tare da bibiyar kafofin watsa labarai domin sanin abin da ke faruwa, sannan su lura da yanayin tsaron kawunansu.

Su ma Birtaniya da Canada sun fitar da irin wannan sanarwa ta jan hankalin ‘yan kasar su da su shafa wa kawunansu lafiya a yayin da ake zanga-zangar.

Masu shirya zanga-zangar, mai taken #EndBadGovernance a Turancin Ingilishi, sun sha alwashin gudanar da ita domin matsa lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo rangwame game da matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaro da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: