Zulum ya kudiri aniyar mayar da yan gudun hijira

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, a jiya ya kaddamar da wasu kwamitoci guda biyu da zasu tabbatar da komawar yan gudun hijira zuwa kananan hukumomin jihar da aka yanto.

Tuni gwamnati a watan da ya gabata ta fara aikin mayar da yan gudun hijiran daga babban birnin jihar, Maiduguri, da sauran kananan hukumomi, zuwa garuruwansu na ainihi.

Rikicin da ake cigaba da yi a Arewa maso Gabas kawo yanzu ya raba mutane miliyan 2 da dubu 700 da gidajensu, a cewar wani rahoton hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.

Daga cikin wannan adadin, kimanin kashi 80 cikin 100 sun fito ne daga jihar Borno, inda nan ne jihar da rikicin na sama da shekaru 10 yafi kamari.

Jihar Borno tana da sansanonin yan gudun hijira na gwamnati guda 32, da wasu wadanda bana gwamnati ba, wanda ba san adadinsu ba, kuma suke dauke da mafiya yawan yan gudun hijira.

Boko HaramBornoINSECURITYZULUM
Comments (0)
Add Comment