Gwamnan jihar jigawa Malam Umar Namadi ya bayyana cewa masu zuba jari suna da gazawa wajen samun ci gaba a jihar Jigawa saboda wasu manufofin gwamnatin tarayya da kuma bukatu na bayar da lasisi da za su fi dacewa ga masu zuba jari.
Gwamna Namadi ya bayyana yadda jihar ta yi rashin samar da ayyuka sama da 50,000 na masu zuba jari a jihar a lokacin taron koli na tattalin arzikin kasa karo na 29 da kungiyar tattalin arzikin Najeriya NESG ta shirya jiya litinin a Abuja.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa samar da magudanar ruwa zai amfani manoma har na makwabta, inda cewa kamfanin yana son budadden magudanar ruwa a matsayin tushen ruwansu na farko, amma gwamnatin tarayya ta ba da lasisin bututun ruwa kawai.
Ya bayyana cewa, masu zuba jarin za su dauki shekaru goma kafin su dawo da jarin da suka zuba, yayin da za su dauki shekaru biyar idan suka zuba jarin.
Gwamna Namadi ya ce jarin zai taimaka wa jihar wajen samar da ayyukan yi kai tsaye guda dubu 50.