A wani labarin kuma, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC kawo yanzu ta tabbatar da mutuwar mutane 185 wanda zazzabin Lassa ya hallaka a kasar nan a shekarar 2020.
A makon da ya gabata, yawan mutanen da cutar ta kashe 176 ne.
A wani rahoton halin da ake ciki, wanda cibiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo jiya Alhamis, cibiyar tace an samu bullar zazzabin a jihoshi 27 na kasarnan, a fadin kananan hukumomi 126.
Cibiyar tace yawan mutanen da zazzabin ya harba sun karu zuwa 951 a satin nan, kari daga 932 a satin baya.
Tace jihar Edo ita ce kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da zazzabin, inda jihoshin Ondo da Ebonyi suka biyo baya.
Najeriya ta jima tana fama da zazzabin Lassa, wanda ya yanzu ya zamo annoba.
Kusan kowace shekara ana samun barkewar zazzabin.