Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya faɗi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing.
Buhari ya yaba wa ƙasar Birtaniya kan tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama, musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ƴan tayar da ƙayar-baya ya ɗaiɗaita.
Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, inda ya ce dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa.
Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyar ta ce ba ta jin daɗi barin Najeriya da za ta yi, musamman ma ganin cewa ta saba da abubuwa da dama a ƙasar, kamar al’adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi.
Ta kuma yaba wa shugaba Buhari kan samun nasarar kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas, inda ta ce ya yi kokari matuka wajen tafiya da ƴan ƙasar gaba-ɗaya.