Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce zai iya rantsewa da Ƙur’ani bai saci kuɗi ba a lokacin da yake mulkin jihar.
Ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan rediyon Freedom da ke Kaduna a ranar Talata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majalisar Jihar Kaduna dai tana binciken tsohon gwamnan ne bisa zargin karkatar da sama da naira biliyan 324 a zamaninsa, zargin da tsohon gwamnan da waɗanda suka aiki tare suka ƙaryata.
A cewarsa, “Na yi shiru ne domin ganin yadda za ta kaya. Ina yawan addu’ar Allah Ya min jagora a duk abin da nake yi a rayuwa. A matsayina na ɗan Adam, ina ƙoƙari wajen guje wa cin amanar mutane ko kuma aikata wani abu da bai dace ba.
“Na sha faɗa cewa duk lokacin da tsofaffin gwamnonin Kaduna da sauran shugabanni suka yarda a yi rantsuwa da Ƙur’ani cewa ba su saci kuɗin al’umma ba, to nima a shirye nake saboda na san ban shiga siyasa domin sata ba. Na shiga siyasa ne domin hidimta wa al’umma.
“Amma akwai ban mamaki abin da ke faruwa, amma haka rayuwa take. Abin da zan ce kawai shi ne duk wani bita da ƙulli da ƙarairayi da ake laƙa mana a cigaba domin mun kai kukarmu wajen Allah.”
El-Rufai ya ce bayan karatun da yake yi, zai dawo siyasa dumu-dumu a shekarar 2027 saboda a cewarsa ba a yin ritaya a siyasa.