Zaben Amurka: Mutum Miliyan 32 sun kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen farko

Masu zaɓe fiye da miliyan 32 sun kaɗa ƙuri’arsu a sahun farko na zaɓen na bana kamar yadda ɗakin sa ido kan zaɓe na jami’ar Florida.

Kimanin mutum miliyan 15 na waɗanda suka yi zaɓen na wuri za ta kaɗa ƙuri’ar a rumfunan zaɓe, inda kuma kimanin miliyan 17 suka yi zaɓen ta hanyar gidan waya.

Wannan zaɓen na wuri dai na zuwa saura kimanin mako guda a kaɗa ƙuri’ar gamagari abin da ke nufin za a ci gaba da samun ƙaruwa da raguwar alƙaluma ga dukkannin ƴantakarar.

Ƴan jam’iyyar Democrat sun fi kaɗa ƙuri’ar ta hanyar saƙon gidan waya. To amma a shekarar 2024, ƴan jam’iyyar Republic suna ta ƙaoƙarin ƙwarara wa ƴan jam’iyyarsu gwiwa da su ma su yi zaɓen ta gidan wayar.

A 2020 ƴan Republican sun soki kaɗa ƙuri’ar ta gidan waya inda suka ce wata hanya ce ta maguɗi. Sai dai bincike da aka gudanar ya nuna cewa da wuya a samu maguɗi ta hanyar idan dai ban da wasu ƴan lokuta da akan iya samun hakan.

  • BBC Hausa
Comments (0)
Add Comment