Za’a Hana Almajirai Bara a Jigawa Saboda Korona

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce zata samar da karin kayayyakin abinchi ga makarantun Tsangaya domin hana almajirai barace-barace a jihar nan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka a jawabin da ya yiwa al’ummar jihar nan dangane da samun rahotan bullar cutar corona.

Ya ce gwamnatin jiha ta killace yara almajirai su dari shida da sittin da shida da aka dawo dasu daga jihohin Kano da Gombe.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce gwamnati tana shirin yiwa almajiran da aka dawo dasu gwaji na bai daya kafin mayar dasu ga iyayen su.

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar


Daga nan sai ya yabawa kungiyoyin da dai-daikun mutane bisa hadin kai da tallafin da suke baiwa Gwamnatin Jiha wajen yaki da cutar covid-19.

Tallafi na baya-bayanan na naira miliyan ashirin ya fito ne daga Alhaji Dahiru Mangal wani dan kasuwa da kuma ofishin jakadancin kasar China wanda ya bada gudummawar naira miliyan takwas da dubu dari hudu.

BadarucoroCOVID - 19Jigawa
Comments (0)
Add Comment