Za’a binciki Kamfanin Sterling Oil Exploration kan zargin na gudanar da aiki maras inganci

Majalisar wakilai zata fara bincike kan zargi da ake yiwa Kamfanin Sterling Oil Exploration na gudanar da aiki maras inganci a jihar Akwa Ibom.

Wannan ya biyo bayan korafi da wata kungiya mai sanya ido da wayar da kai ta gabatar a gaban majalisar.

Korafin wanda dan majalisar David Umar na jam’iyyar PDP daga Jihar Kaduna ya gabatar a gaban majalisar,ya zargi Kamfanin da yin aikin kwangila mai cike da ha’inci da kuma wasu zarge-zarge. Da yake jagorantar zaman majalisar na jiya mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu,ya gabatar da korafin ga kwamitin karbar korafe-korafen jama’a domin yayi bincike.

Comments (0)
Add Comment