A gobe ne ake saran zaman tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kwararrun masana masu ruwa da tsaki da kungiyoyi a bangarn lafiya dangane da yajin aikin da ‘yan kungiyar lokitoci masu neman kwarewa suke ciki a yanzu haka.
Mai Magana da yawun ma’aikatar Ayyuka da samar da aikinyi ta kasa Charlse Akpan ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai ayau litinin a Abuja.
Zaman sulhun da ake saran ministan ayyuka da samar da aikinyi na Kasa Chris Ngige zai jagoranta a dakin taro na ofishinsa da karfe 2 na gobe Talata.
Duk kuwa da cewa b’a kaiga biyawa ‘yan kungiyar buqatun suba, bayan wa’adin kwanaki goma 15 din da kungiyar likitoci masu neman kwarewar ta baiwa gwamnatin tarayyar na ta biya su dukkanin alawaus-alawus dinsu da sauran buqatu gabanin ta janye yajin aikin.
Hakan na zuwane mako guda, bayan da kungiyar Likitoci ta kasa da tayi barazanar shiga nata yajin aikin gama gari, muddin ba’a gwamnatin tarayya bata cika alkawuran data daukarwa kungiyar ba, yayin mabambamta zama datayi da wakilan kungiyar.