Za a yi amfani da bayanan rijistar jihohi wajen rabon tallafin rage radadin cire tallafin man fetur

Majalisar tattalin arziki ta kasa a jiya tace za a yi amfani da hanyar bayanan rijistar jihohi wajen rabon tallafin rage radadin cire tallafin man fetur.

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, shi ne ya sanar da hakan a jiya alhamis yayin taron majalisar wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shatima ya jagoranta a zauren majalisar dake fadar shugaban kasa.

Taron ya samu halattar gwamnonin jihohi 36 da daraktocin kungiyar gwamnoni da masu ruwa da tsaki daga asusun bankin duniya da sauran hukumomin gwamnati.

Yan Najeriya dai sun kalubalenci shirin bada tallafin rage radadin cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya bullo da shi, inda suke ganin cewa hanya ce kawai da wasu jami’an gwamnati za suyi amfani da ita wajen sace kudaden.

Hakan ce ta sanya shugaban kasar yace za a sake fasalin shirin bada tallafin.

Comments (0)
Add Comment