Za a kammala sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano cikin wata 14 – Ministan ayyuka

Za a kammala sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano cikin wata 14 – Ministan ayyuka

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake ƙaddamar da aikin sabunta titin Abuja-Kaduna-Kano.

Da yake jawabi a madadin shugaban a wajen ƙaddamar, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana titin a matsayin mai muhimmanci, wanda ya ce yana haɗa babban birnin tarayyar ƙasar da sama da jihohi 12 a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da arewa ta gabashin ƙasar.

A wajen taron wanda aka yi a garin Jere da ke ƙaramar hukumar Kagarko, Uba Sani ya ce an yi watsi da hanyar na tsawon lokaci, wanda hakan a cewarsa ya jawo asarar rayuka da illata tattalin arzikin ƙasar.

“Sabunta wannan titin zai sauƙaƙa zirga-zirga, sannan zai samar da ayyukan yi tare da inganta tsaro da walwalar al’umma,” in ji shi kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Ya ce abin da ya jawo tsaikon aikin a baya shi ne rashin tsaro, wanda ya ce yanzu ana samu nasara a ɓangaren, inda ya ce matafiya suna tafiya a kowane lokaci ba tare da fargaba ba.

A nasa ɓangaren, ministan ayyuka, David Umahi ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Kaduna wajen tabbatar da an ci gaba da aikin, inda ya tabbatar da cewa za a kammala aikin a cikin wata 14.

Comments (0)
Add Comment