za a cire tallafin man fetur kafin saukar shugaba Buhari.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed, a makwanni biyun da suka gabata a wata ziyarar ban girma da ta kai hedikwatar muryar Najeriya da ke Abuja, ta bayyana cewa za a cire tallafin man fetur kafin karshen wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar 29 ga watan Mayu.

Ta danganta jinkirin cire tallafin, kamar yadda dokar masana’antar man fetur ta tanadar a shekarar 2021, ga babban zaben 2023 da kuma kidayar al’ummar kasa.

Karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa Clement Agba, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar a ranar 15 ga watan Maris, ya ce har yanzu ba a cimma matsaya kan yadda za a rage illar da shirin cire tallafin man fetur zai yi wa ‘yan kasar ba.

Ya ce duk da cewa kwamitin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya kwashe kusan shekara guda yana aiki, amma ba a cimma matsayaba.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, a ranar Talata ya ce gwamnati za ta mikawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu aiwatar da matakan rage tallafin man fetur.

To Sai dai jami’an kwadago sun bayyana shirin da gwamnatin Buhari ke jagoranta na cire tallafin kafin ta tasauka a ranar 29 ga watan Mayu, sannan a bar hargitsin da zai biyo baya da gwamnatin mai jiran gado inda tace bai dace.

Shugaban TUC, Osifo, ya ce dole ne a tattauna tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati  ko mai fita ko mai jiran gado kafin cire tallafin. ‘Yan Najeriya sun damu da rashin tabbas game da shirin cire tallafin na irin halin da zasu shiga.

Comments (0)
Add Comment