Mataimakin shugaban kasa, Sen Kassim Shettima ya ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake da aka kai garin Gwoza a jihar Borno ya ƙaru zuwa 32.
Shekttima ya sanar da haka ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya jihar ta Borno game da ibtila’in da ya faru.
Ya ƙara da cewa cikin mutane 42 da aka kai asibiti bayan harin, an sallami mutane 14.
A cewarsa, har yanzu mutane 26 na samun kulawar likitoci.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bai wa dukkanin mutanen da ibtila’in ya rutsa da su tallafin kuɗi tare da yi wa iyalan waɗanda suka mutu jaje.