Majalisar dinkin duniya ce ta kebe ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya, domin ilimantar da jama’a game da illar da miyagun kwayoyi ke haddasawa a cikin al’umma.
Wannan rana ta samu goyon bayan daidaikun jama’a da daukacin al’umma da sauran kungiyoyi a dukkan fadin duniya. A hannu guda kuma, ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka (UNODC) ya tsara shirye-shiryen Ilimantar da jama’a game da yaki da wannan matsala daga dukkan fannoni.
Ofishin na UNODC ya kuma bayyana cewa, kusan mutane miliyan 200 ne ke ta’ammali da miyagun kwayoyi, wadanda suka hada da hodar Iblis. Wannan ya sa MDD ta kebe wannan rana domin kawar da wannan matsala da ta addabin duniya.Masu fashin baki na cewa, galibi matasa ne ke shiga wannan matsala, sakamakon rashin aikin yi ko tasirin abokai, ko rashin tarbiya da sauransu.
Don haka, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su dukufa wajen ilimantar da musamman matasa illar shan miyagun kwayoyi, ta yadda za su kasance masu amfanawa kansu da ma al’umma baki daya.
Bugu da kari, kamata ya yi mahukunta a dukkan matakai, su gindaya tsaurara ka’idoji game da yadda za a rika sayar da wasu nau’o’in magunguna ga jama’a, don hana shagunan sayar da magunguna, sayarwa mutane wasu magunguna dake iya yin illa ga lafiyar bil-Adama ba tare da iznin likita ba.