‘Yansanda sun fara bincike akan mutuwar Abdulkarim Na Allah, duk da kasancewar gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana lamarin da mai kama da kisan kai.
Mamacin da ne a wajen Sanata Bala Na’Allah.
Kwamishinan yansanda na jihar Kaduna, Mudasiru Abdullahi, ya bayar da umarnin bincike akan lamarin.
Kwamishinan ya bayar da umarnin a daren jiya a Kaduna, cikin wata sanarwa da kakakin yansandan jihar, Mohammed Jalige, ya fitar.
An rawaito cewa an kashe matukin jirgin sama mai shekara 36 jiya a gidansa dake Kaduna.
‘Yansanda sun nemi jama’ar gari da su taimaka da bayanai masu muhimmmanci dangane da binciken kisan kan.
A nasa bangaren, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana matsayar gwamnatin jihar cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.