‘Yansanda na tarwatsa masu zanga-zangar Take it Back a Najeriya

‘Yansanda na tarwatsa masu zanga-zangar Take it Back a Najeriya

Wasu matasa a ƙarƙashin ƙungiyar Take It Back Movement sun fara gudanar da zanga-zanga a wasu a jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Cikin jihohin da ake gudanar da zanga-zangar yanzu haka akwai jihohin Legas da Oyo da Rivers, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Omoyele Sowore – wanda shi ne ɗantakarar jam’iyyar AAC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 – shi ne shugaban ƙungiyar Take it Back kuma ya fito a zanga-zangar.

Matasan sun fito zanga-zangar ce duk da shawarar da rundunar ƴansanda ta ba su cewa su dakatar da yunƙurinsu saboda ranar ta dace da ranar ‘yansanda ta ƙasa.

Rahotanni na cewa matasan sun fito a ƙarƙashin gadar Ikeja da ke Legas, inda suka ratsa unguwannin birnin jihar suna raira waƙoƙi.

Rahotanni daga Fatakwal sun ce ƴansanda na harba hayaƙi mai sa hawaye tare da tarwatsa masu zanga-zangar.

-BBC Hausa

Comments (0)
Add Comment