Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da kamen mutum 143 da ake zargi masu satar mutane ne da kuma yan fashi a wurare daban daban na jihar a tsukin wata biyu. Kwamishinan yan sandan jihar, Audu Dabigi ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a hedikwatar rundunar inda ya ce an gano wasu manyan makamai daga hannun mutanen. Mutanen da aka kama sun hada da yan fashi 73 sai yan bindiga 70 ciki har da wanda ake nema ruwa a jallo da aka damke a lokacin da yake kokarin hada wa yan bindigar wani tsubbu domin gudanar da ayyukansu.Ya kara da cewa yan sandan sun halaka yan bindiga tara cikin wata biyu da suka gabata. Dabigi ya ce cikin makaman da aka gano a hannun mutanen da ake zargi sun hada da bindiga kirar AK47 da wasu bindiga kirar gida da kuma alburusai da dama. Ya kara da cewa an sake kama mutum 985 da ake zargi masu satar waya ne da yan fashi takawas da kuma wani da ake zargi da satar kaya a tashar jirgin kasa.