Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobin ta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.
Shugaban kungiyar ta kasa Baba Usman Ngelzerma ya ce wannan rikici ya barke ne tun a ranar juma’a sakamakon harin da tawagar ‘Yan sa-kan suka kai matsugunan makiyayan, abinda ya kai ga rasa rayuka da kuma kona rugagen Fulanin.
Ngelzerma ya ce daga cikin matsugunan Fulanin da aka kaiwa hari sun hada da Tsola da Asara da Karan biki da kuma Sakamaro duka a yankin Gwadabawa, kuma an jikkata mutane da dama.
Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga barayin shanu, abinda ya sa wasu al’ummomi suka kafa kungiyoyin Sa-kai domin taimakawa jami’an tsaro kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
Lokaci zuwa lokaci ana samun arangama tsakanin Fulani makiyayan da ‘Yan sakai abinda ke kaiga rasa rayuka.