‘Yan majalisar wakilai sun musanta zargin karɓan ₦100M a matsayin kuɗin rage raɗaɗi cire tallafi

Majalisar wakilan Najeriya ta musanta zargin da ke cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin kuɗin rage raɗaɗi cire tallafi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar ya bayyana iƙirarin – da mataimakin sakataren gamayyar ƙungiyar ƙwadogon ƙasar NLC, Christopher Onyeka ya yi, a matsayin zargi marar tushe.

Mista Onyeka ya yi zargin cewa kowane ɗan majalisa ya karɓi naira miliyan 100 daga gwamnatin tarayya a matsayin tallafin rage raɗaɗi.

Sanarwar ta Mista Rotimi, ta kuma buƙaci mataimakin sakataren NLC da ya fito ya nemi afuwar majalisar a bainar jama’a

Sanarwar ta bayyana iƙirarin a matsayin zargi marar tushe bare makama.

Mista Rotimi, ya ƙara da tunasar da kungiyar NLC da duka ‘yan Najeriya cewa a cikin ƙasa da kwana 100 da ƙaddamar da majalisa ta 10, majalisar ta yi ƙoƙari wajen inganta jin daɗi da walwalar ma’aikata da sauran Najeriya.

Comments (0)
Add Comment