‘Yan kasuwan Arewacin Nigeria suna asarar kimanin Naira biliyan 13 a duk mako

‘Yan kasuwan Arewacin Nigeria sun koka akan yadda suke asarar kimanin Naira biliyan 13 a duk mako, sakamakon rufe iyakokin kasar da aka yi da Jamhuriyar Nijar.

Idan zamu iya tunawa dai shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 4 ga watan Agustan da ya gabata ne, ya bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin kasarnan da jamhuriyar Nijar.

Iyakokin sun hada da Jibiya a jihar Katsina, Illelah a Sokoto da Maigatari a Jigawa.

Da yake zantawa da manema labarai jiya a Abuja, shugaban kungiyar Arewa Economic Forum Ibrahim Yahaya Dandakata, yace rufe iyakokin kasar nan ya haifar illa ga tattalin arziki, wanda ya kara haifar da rufe kasuwannin dake makwabtaka da kasashen biyu.

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta bude iyakar maje-illo dake jihar Kebbi domin baiwa ‘yan kasuwa damar shigowa da kayayyaki zuwa kasar nan. Shima da yake nasa jawabin, wani dan kasuwa kuma memba a dandalin Hamza Saleh Jibiya, yace tun bayan rufe iyakokin, akwai kimanin kwantena 2,000 da ke makare da kayayyaki wadanda tuni wasu daga cikin su suka lalace wasu kuma suke jiran ko ta kwana.

Comments (0)
Add Comment