’Yan kasuwa sun goyi bayan NNPC ta sayar da danyan man fetur ga matatun kasar nan

A jiya Laraba ’yan kasuwar mai da iskar gas a karkashin kungiyar masu samar da mai da iskar gas ta kasa (NOGASA), sun goyi bayan hukuncin da gwamnatin Bola Tinubu tayi kan umarnin da ta ba kamfanin man fetur na kasa (NNPC) na sayar da danyen mai a naira ga matatun man Kasar nan.

Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a Abuja, Shugaban kungiyar na kasa, Mista Benneth Korie, ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da fasa kwaurin albarkatun man fetur a kan iyakoki.

Korie ya bayar da hujjar cewa, magance kalubalen fasakwauri, da inganta harkar noma a da kuma inganta hanyoyin sufuri a kasar, da magance yawan haraji zai taimaka wajen sake gina tattalin arzikin kasar. A cewarsa, abin da ke da muhimmanci ga kungiyar shi ne samar da albarkatun man fetur, inda ya bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa an samar da danyen mai ba ga manyan matatun man fetur kadai ba har ma da matatun mai na zamani.

Comments (0)
Add Comment