Mai shari’a Joy Uwanna an sace ta ne yayin da take komawa gida bayan ta tashi daga Kotu ranar Litinin, a hanyar Uyo zuwa Okoboin dake garin Oron.
An rawaito cewa ‘Yan bindigar sun budewa alkaliyar wuta tare da kashe dan Sanda dake mata rakiya, daga bisani suka yi awon gaba da ita.
Kakakin ‘Yan sandan Jihar Akwa Ibom Odiko Macdon, yace bayyana wannan hari da mummuna, yana mai cewa jami’an tsaro na cigaba da bincike domin gano inda alkaliyar take. Kawo yanzu dai babu wata kungiya suka dauki alhakin kai wannan hari, yayinda ake samun yawaitar sace mutane domin karbar kudin fansa a fadin kasar nan.