Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 a jihar Kaduna.

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 10 a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar Kaduna tace ta samu rahotan daga hukumomi tsaron cewa anyi garkuwa da dalibai 10 a Kachia.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, rahotan da aka samu an sace daliban makarantar jeka ka dawo take Kachia a jiya litinin.
Kawo yanzu dai ba’a kai ga gano wadanda sukayi garkuwa da daliban ba,amma dai ana cigaba da bincike a harabar makarantar.
Samuel Aruwan, ya kuma yi alkawarin cigaba da bibiyar lamarin domin sanar da al’umma halin da ake ciki.

Comments (0)
Add Comment