Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun halaka wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jigawa, Zahraddeen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce maharan sun kai wa gidan mahaifin Sabo hari da tsakar daren Laraba, inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma ɗan uwansa.
Zahraddeen ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun harbi Yusuf a ƙirji kuma ya rasu ne bayan an garzaya da shi asibitin Birnin Kudu.
“Da misalin ƙarfe 3:25 na daren Laraba, ‘yan sandan Birnin Kudu sun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai cikin gidan Alhaji Abubakar mai shekara 50 a Kawo, suka harbi ɗansa a ƙirji mai suna Sabo Yusuf mai shekara 25,” in ji Zahraddeen Aminuddeen.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tura rundunar yaƙi da fashi da makami zuwa yankin.