’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wata rundunar tsaro a jihar Sakkwato

’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani hari da suka kai wa sansanin rundunar tsaron hadin gwiwa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Binciken manema labarai ya gano cewa kafin wayewar garin Juma’a ne ’yan bindiga suka kai hari a kan sansanin tsaron hadin gwiwa da ke kauyen Dama, inda suka kona motocin soji biyu suka kuma sace wata motar da suka yi amfani da ita wajen daukar kayan abincin sata.

Da yake tabbatar da harin, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir, wanda aka fi sani da Danchadi, ya ce wasu daga cikin jami’an tsaron sun bace.

Comments (0)
Add Comment