Yan bindiga sun kai hari wani masallaci a garin Sabon Birni

Yan bindiga sun kai hari  wani masallaci da ke kauyen Bushe, karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun sace akalla mutane goma daga cikin masu ibada, ciki har da limamin masallacin.

Shaidu sun bayyanawa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin masallacin ne a ranar Alhamis, yayin da masu ibada ke gabatar da sallar asubahi.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun dade suna gallaza wa al’ummar garin duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin.

Sun ce daukin gaggawa da sojojin suka kawo ya taimaka wajen takaita barnar da ‘yan bindigar za su yi.

Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ta tabbatar da harin a jiya Juma’a.

Kakakin rundunar, Ahmed Rufai, ya ce hukumomin ‘yansanda suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin kubutar da wadanda aka sace.

Wani dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Sabon Birni  ya kuma tabbatar da faruwar lamarin.

Comments (0)
Add Comment