Gwamnatin Filato ta ce wasu ’yan bindiga da ke addabar al’umomin karamar hukumar Wase da ke jihar sun mika mata bindigoginsu kirar AK47, bayan wata tattaunawar sulhu.
Mai bai wa Gwamna Caleb Mutfwang shawara na musamman a kan harkokin tsaro kuma kwamandan Operation Rainbow, Birgediya Gakji Shippi, ya ce mika makaman ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da ’yan bindigar.
Ya ce baya ga bindigogi kirarAK47, ’yan bindigar sun mika wasu nau’ukan makaman, wanda hakan ke nuna aniyarsu ta samar da zaman lafiya ta hanyar kwance damara.
Ya kara da cewa, ’yan bindigar ba su mika bindigogin kai tsaye ba saboda fargaba, amma sun yi hakan ne ta hanyar masu shiga tsakani yayin tattaunawar.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokarin karfafa gwiwar ’yan bindigar su mika makamansu bisa radin kansu.