Kungiyar yan achaba ta jihar Kebbi ta nemi kariyar jami’an tsaro bayan barayi sun kashe yayan kungiyar hudu a jihar.
Shugaban kungiyar, Nafi’u Zaki, yayi kiran yayin wata ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Birnin Kebbi.
Nafi’u Zaki yace an kashe yayan kungiyar hudu a karamar hukumar Birnin Kebbi ta jihar.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Yace ana tsayar da mutanensu a dake su, wasu lokutan a yanke da wuka a kashe su.
Yace kafin yan kwanakinnan, kungiyar bata da rahoton wani dan kungiyar da aka kashe a kokarin kwace masa babur.
Nafi’u Zaki yace kungiyar tana da mambobi wadanda suka yi rijista su dubu talatin da bakwai, inda ya kara da cewa dayawa daga cikinsu sun fito daga kauyuka da jihoshi makota.