Yakin da ake yi tsakanin sojojin dake gaba da juna a sudan ya fantsama zuwa yankin port Sudan, karo na farko kenan da samun rikin a yankin tun faro yakin sama da watanni 5.
Sojojin sudan sunyi musayar wuta da wasu sojojin hadin gwiwa na kasar.
Dakarun sunyi kokarin janye shinge daka sojojin yankin suka kafa a tsakiyar birnin.
Port sudan shine birnin da jami’an gwamnatin da hukumomin majalisar dinkin duniya suka kaura biyo bayan rikicin da ya dai-daita babban birinin kasar Khartoum. Rikici tsakanin sojin sudan da dakarun kai daukin gagagwa na RSF,yayi sanadiyyar mutuwar mutane da raba dubban mutane da muhallan su tun bayan fara yakin a watan Afrilu.