Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani mahaifi da ƴaƴansa maza biyu a yayin da suke dawowa daga gona a garin Ore da ke Ƙaramar Hukumar Ado ta Jihar Benue a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu sassa na Ado da ke makwaftaka da Jihar Ebonyi inda ake ta samun rikice-rikicen kan iyaka.
Haka kuma rahotanni na cewa a baya an ta samun hare-haren makiyaya a yankin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan kisan ya sa ba su iya fita su yi walwala yadda ya kamata.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ado, James Oche ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin hakazalika shi ma mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Benue ya tabbatar da hakan.