Yadda Sojoji Suka Dakile Yunkurin Kai Hari Kusa Da Filin Jirgin Sama Na Kaduna

Da sanyin safiyar ranar Lahadi ne ’yan bindiga suka yi yunkurin sake sace mutane a unguwar ma’aikatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da ke Kaduna.

Akalla mutum 12 ne suka sami nasarar sacewa bayan sun shiga unguwar ta karfin tsiya da misalin karfe 2:00 na dare.

Unguwar dai na dab da filin jirgin sama na Kaduna.

Daga cikin wadanda aka sace yayin harin da aka kai a makon jiya akwai ma’aikacin Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) tare da iyalansa da kuma wata mata da ‘ya’yan wani ma’aikacin Hukumar Kula da Harsashen Yanayi ta Kasa (NiMET).

‘Yan bindigar dai wadanda suka suka sake dawowa unguwar ranar Lahadi sun fuskanci tirjiya daga dakarun sojin sama da na kasa.

Wani jami’in hukumar ta FAAN wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya ce maharan sun biyo ta wata barauniyar hanya ne.

“Sun biyo ta wata hanya ne ba ta bangaren filin jirgin ba, amma sun yi rashin sa’a jami’an tsaro a shirye suke.”

Wani mazaunin unguwar ya ce ‘yan bindigar na hankoron kai harin ne wani gida kafin jami’an tsaron su ci karfinsu.

Comments (0)
Add Comment