Yadda Sarkin Musulmi Ya Yi Wa Wasu Manyan Najeriya 20 Nadin Sarauta


Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi wa wasu manyan mutane akalla 20 nadin sarauta a ranar Lahadi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an yi nadin sarautar ne a fadar Sarkin Musulmin da ke birnin Shehu.

A jawabansa yayin bikin nadin, Sultan na Sakkwato ya hori wadanda aka yi wa sabbin nadin sarautar da su jajirce wajen rike sauke nauyin da ya rataya a wuyansu bisa la’akari da manufofin da Shehu Mujaddi ya kafa masarautar.

Sarkin ya ce wannan bikin nadin sarautar wanda shi ne karon karfo a tarihi, yana sake dawo wa da kuma karfafa martabar Marigayi Shehu Usman Dan Fodiyo.

“Wannan nadin sarauta da kuka samu wata babbar daraja ce da kuma dama ta yi wa al’umma hidima da ma masarautar Sakkwato baki daya.”

“Kuma ina tsammanin dukkanku za ku sauke wannan nauyi tare ta hanyar kwazo da himma musamman a yayin da wata Ramadan ke karatowa wajen amfanar da Musulmi.”

Ina kuma kiran al’umma da su ci gaba da yi mana addu’a domin tabbatar da adalci yayin sauke nauyin jagoranci da rataya a wuyanmu,” in ji Sarkin Musulmi.

Mafi shahara daga cikin wadanda aka yi wa nadin sarautar akwai ’ya’ya uku na Sarkin Musulmi na 18, Marigayi Ibrahim Dasuki.

Sun hada da tsohon dan majalisar tarayya mai zaman kwamishinan Kudi a Jihar Sakkwato, Abdussaman Dasuki a matsayin Santukarkin Sakkwato.

Akwai kuma Abubakar Dasuki a matsayin Danmaje da Alhaji Khadir Dasuki a matsayin Durbi.

Sauran manyan kasar da aka yi wa nadin sun hada da Shugaban Hukumar Alhazai na Jihar Sakkwato, Alhaji Muhtari Maigona a matsayin Zanna, sai tsohon Gwamnan Kogi, Alhaji Ibrahim Idris a matsayin Jekada.

Sauran sun hada da tsohon Ministan Sufuri Alhaji Yusuf Suleiman a matsayin Dan’amar da Farfesa Ahmad Mora a matsayin Kayayen Sarkin Musulmi da Alhaji Musa Bashar a matsayin Mayana.

Tsohon Darekta a Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), Alhaji Faruk Ahmada a matsayin Danmadami da kuma Alhaji Jelani Aliyu, Shugaban Hukumar Kere-Keren Ababen Hawa a Najeriya (NADDC).

Asalin labarin;

https://aminiya.dailytrust.com/sarkin-musulmi-ya-yi-wa-wasu-manyan-najeriya-20-nadin-sarauta

MUSULUNCI
Comments (0)
Add Comment