Yadda Aka Kama Wata Mata Da Ke Shayar Da Maciji Nononta

Mazauna kauyen Nenohwe sun shiga cikin zullumi bayan samun wata mata a gidan kawarta tana shayar da wani kasurgumin maciji nononta.

Kafar labarai ta The Manica Post ta ruwaito cewa, wata yarinya mai shekara 12 ta hango matar mai suna Gogo Nenohwe tana shayar da wani katon maciji nononta.

Yarinyar ta ce a daidai lokacin kuma tsohuwar tana furta wa macijin sunayen wadansu mutanen kauyen da macijin zai je ya yi musu illa.

Wadansu mata biyu dattawa kuma kawayen matar da ake zargin da suka hada da Gogo Sabie Nenohwe da Gogo Ethel Sithole da suke zargin matar da yin tsafi, an gurfanar da su a gaban kotun Mutambara kan zargin yin tsafi.

Wacce ta gani da idonta, ta bayyana wa kotun da ke kasar Zimbabwe a ranar Asabar 13 ga Maris 2021 cewa: “Na ga Gogo Nenohwe tana shayar da wani kasurgumin maciji, tana sanye da tufafi launin ja tare da sarka.

“Bayan shayar da macijin, ta dauko wani farantin abinci tana ciyar da macijin.

“Ban gano abincin da take ci ba, amma na ji tana gurnani tana kiran sunayen mutanen kauyen tana fada wa macijin ya yi musu illa.”

Dagacin kauyen mai suna Molline Nenohwe wanda aka sanar masa da abin da ke faruwa, ya mika koke ga Alkalin Kotun Mutambara.

Daga nan aka gayyaci kawayen tsohuwar zuwa kotun gargajiya don yin bayani.

’Yar dangin wacce ake zargi ce, ta ce, “Ina kwance a dakin da za a iya ganin Gogo Nenohwe tana shayar da maciji nononta.

“Macijin yana zama a wannan dakin. Hakan ya sa na daina zama a cikin dakin na roki ’yar uwata ta mai da ni zuwa wani dakin.

“Wani lokaci macijin yana fitowa daga cikin kwando da rana.”

Ita dai Gogo Nenohwe lokacin da manema labarai ke neman karin bayani, bayan shigar da karar a kotu ta ki cewa komai.

MACEMACIJISHAYARWA
Comments (0)
Add Comment