Ya kamata malamai su rika samun Naira 250,000, N500,000 da kuma Naira miliyan 1 a duk wata

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan ilimin jami’a Abubakar Fulata, ya yi kira da a kara albashi ga malaman firamare da sakandare da jami’o’i.

Shugaban ya ce ya kamata malamai su rika samun Naira 250,000, N500,000 da kuma Naira miliyan 1 a duk wata.

Fulata yana magana ne a wajen wani taron bita na kwana guda na masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa taswirorin tsarin ilimi na Najeriya na (2023-2027), a Abuja jiya Alhamis.

Fulata ya ce yana da kyau malaman Najeriya su kara kwarin gwiwa ta hanyar biyan su kudaden da suka dace domin koyar da yaran.

Ya kuma jaddada wajibcin fassara dukkan litattafan darussa zuwa harsunan cikin gida. A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun yi kokari a fannin ilimin kasar amma hakan bai haifar da sakamakon da ake so ba.

Comments (0)
Add Comment