Kungiyar mai zaman kanta da ake kira Islamic Society of Eggonland (ISE) ta ba da abinci da darajarsa ya kai miliyoyin Naira ga fursunonin da ke karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa.
Babban sakataren kungiyar ta kasar Ingila, Umar Abdullahi Galle sa’ad da yake ba da kayan, ya ce abincin ya ƙunshi: buhu biyar na shinkafa, buhu biyu na alkama, buhu biyu na alkama, buhun sukari biyu, buhun gishiri guda 1, sauran sun hada da kwali biyu na kifi, kwali 2 na Maggie cube da kuma jarkar mai.