Mutum guda ya rasa ransa, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan wata iska mai karfi data afku a yankin Agbashi dake karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.
Sama da gidaje 100 ne suka rushe lokacin da iskar mai karfin gaske ta afku a jiya laraba.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mataimakin shugaban karamar hukumar John Bako, ya bayyana al’amarin a matsayin abin bakin ciki. Yace, wuraren da lamarin ya shafa sun hada da babban masallacin Agbashi da kuma wani bangare na makarantar firamare da kuma sauran wuraren mazauna yankin.