Wasu Yan bindiga sun kashe Malam Dauda Aliyu wani babban Ma’aikaci a Hukumar Bayanan Gidaje ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a yau Juma’a a karamar hukumar Igabi ta Jihar.
An bada rahotan cewa yan bindigar sun je gidan Marigayin ne a kyauyen Barkallahu wanda ya ke da Nisan Kilomita 3 daga cikin birnin Kaduna, inda suka harbe shi.
Rundunar yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai dangane da Lamarin ba, kan ko yana da Alaka da yan fashin Daji.
Yan bindigar sun kuma kaiwa garin da yake Makotaka da garin su Marigayin domin daukar hankalin Al’umma.
Kafin mutuwar tasa, Malam Dauda Aliyu, shine Shugaban Sashen Mulki na Hukumar Tattara Bayanan Gidaje da Filaye ta Jihar Kaduna.