Wasu sun bayyana cewa da dusa da kuma barace-barace suke rayuwa saboda tsananin yunwa

Al’ummar wasu yankunan Zamfara da matsalar tsaro ke daɗa rincaɓewa sun ce da dusa da kuma barace-barace suke rayuwa saboda tsananin yunwa.

Rahotanni na bayyana cewa a yanayin da ake ciki a yanzu, matsalar tsaro ta kai bango a Wanke da Magami da ‘Yar Tasha da Ɗan Sadau da Ɗan Kurmi da dai sauran sassa na jiha.

Kuma galibin mazauna waɗannan ƙauyuka na cewa suna cikin wani hali irin na ni-‘ya-su saboda azaba da hana su sakat da ‘yan bindiga ke yi.

Tsawon sama da shekara goma kenan, mazauna sassan jihar Zamfara, na fama da hare-haren ‘yan fashin daji waɗanda suke auka wa ƙauyuka da garuruwa, inda suke kashe-kashe da jikkata mutane, tare da sace wasu don neman kuɗin fansa daga danginsu.

Wani magidanci da BBC ta tattauna da shi ya ce ”Ba ka isa ka taso daga Gusau ka nufi Magami ba, idan babu rakiyar ‘yan sa-kai ko sojoji.

Rashin fita gonaki da ‘yancin noma, na cikin abubuwan da suka sake kassara mutane yankunan da ma ƙauyukansu.

Monaman da BBC ta tattauna da su, na cewa ba su da ikon yin tafiyar kilomita guda daga garin Magami, sai an sace mutum ko a harbe shi. Manomin ya ce a halin yanzu haka mata da yawa sakin aurensu ake yi saboda rashin abinci, yayin da ƙananan yara suka koma bara.

Comments (0)
Add Comment